Isa ga babban shafi

Amurka ta kara wa'adin visa ga 'yan Najeriyar da ke shiga kasar

Amurka ta sanar da sauyi a tsarin bayar da izinin shiga kasar ga bakin da suka fito daga Najeriya wanda ya bayar da damar kara wa’adi ko kuma tsayin lokacin da bakin za su rika shafewa a Washington ba tare da neman kara wa'adin visa ba.

Dubunnan daruruwan 'yan Najeriya ne kowacce shekara ke balaguro zuwa Amurka.
Dubunnan daruruwan 'yan Najeriya ne kowacce shekara ke balaguro zuwa Amurka. © REUTERS / KEVIN LAMARQUE
Talla

Karkashin sabon tsarin bayar da visar dai ‘yan Najeriya na da wa’adin watanni 60 ko kuma shekaru 5 da za su iya rika shafewa a Amurkan sabanin watanni 24 da suka saba yi a baya.

Sanarwar da ofishin jakadancin Amurka a Najeriyar ya fitar na nuna cewa daga ranar 1 ga watan Maris mai kamawa wannan tsarin tsawaita izinin zama a Amurkan zai fara aiki ga ‘yan Najeriya.

Matakin Amurkan dai baya rasa nasaba da sauye-sauyen da Najeriya ta yi a baya-bayan nan da ya samar da fahimtar juna tsakanin kasashen biyu tare da Fifita bukatar Amurkawa da ke shiga Najeriyar fiya da bakin kowacce kasa.

Shi dai wannan tsarin tsawaita bayar da izinin zama a cikin Amurka ga ‘yan Najeriya ya ta’allaka ne kadai ga masu shiga kasar don yawon bude ido ko kuma don gudanar da harkokin kasuwanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.