An sace wasu Amurkawa 4 a Mexico
Mahukuntan Mexico da na Amurka suna aiki sau da kafa don tabbatar da ceto wasu Amurkawa 4 da wasu ‘yan bindiga suka yi awon gaba da su bayan da suka bude musu wuta a lokacin da suke ketarawa kan iyaka zuwa kasar.
Wallafawa ranar:
Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta FBI ta yi tayin bada dala dubu 50 ga duk wanda ya taimaka wajen gano wadanda aka yi garkuwa da su, tare da kame masu garkuwar.
Ofishin Jakadancin Amurka a Mexico ya ce Amurkawan sun tsallaka garin Matamoros na jihar Tamaulipas ne a cikin wata karamar motar bas mai lambar North Carolina a ranar Juma’a.
Shugaban Mexico, Andres Manuel Lopez Obrador ya ce, rahotannin da ya samu na nuni da cewa wadannan Amurkawa sun shiga kasarsa ne don sayen magunguna, inda suka yi gamo da wadannan gungun masu aikata manyan laifuka.
Ya shaida wa manema labarai cewa mahukuntan Mexico na aiki tare da hukumar FBI ta Amurka don gano mutanen.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu