Yan bindiga sun yi awon gaba da Amurkawa 15 a Haiti
A Haiti ,wasu yan bindiga sun yi awon gaba da wasu ma’aikantan mujami’u 15 yan asalin Amurika a gabshin babban birnin dake Port au Prince.
Wallafawa ranar:
Wata majiya daga yankin na dada nuni cewa daga cikin mutanen da yan bindiga suka yi awon gaba da su akwai ya’an malaman mujami’u daga cikin su.
An dai share shekaru da dama,yan bindiga ne ke cin karnen ba babaka a unguwani dake harabar babban birnin kasar na Haiti,kasancewa gwamnatin kasar ta kasa shawo kan matsallloli da suka jibanci tsaro da kare rayukan al’uma.
Sama da mutane 600 ne yanzu aka gano cewa suna hannun yan bindiga daga farkon shekarar 2021,zuwa tsakiyar shekarar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu