Isa ga babban shafi

Shugaba Andres Manuel Lopez Obrador na shirin sake fasalin siyasar Mexico

Shugaban kasar Mexico Andres Manuel Lopez Obrador ya mayar da hankali ga koken mutanen kasar a yammacin yau Asabar domin kare manufofin siyasar sa da na Mexico da kuma sake fasalin zabensa da ya shafi 'yan adawa da kuma damuwar Amurka, kusan shekara guda kafin zaben wanda zai gaje shi.

Duban yan kasar Mexico yayin zanga-zanga a babban birnin kasar
Duban yan kasar Mexico yayin zanga-zanga a babban birnin kasar AFP - NICOLAS ASFOURI
Talla

Lopez Obrador Shugaban kasar mai ra'ayin rikau na hagu zai yi jawabi a wani gangamin da ya kira a birnin Mexico domin tunawa da cika shekaru 85 da mayar da masana'antar mai ta kasa.

"Dole ne mu tabbatar da 'yancin kanmu, ikonmu,mu tuna da wannan shawara mai cike da tarihi," in ji shi.

Yana magana ne kan kwace wasu kamfanoni na kasashen waje 17 da shugaban kasar Lazaro Cardenas ya zartar a ranar 18 ga Maris, 1938, wanda kuma aka san shi da ba da mafaka ga wasu attajiraoi musaman bangaren Trostky da kuma ‘yan Republican na Spain da suka tsere daga tsarin mulki mai gurguzu na Francoism.

Andres Manuel Lopez Obrador Shugaban kasar Mexico
Andres Manuel Lopez Obrador Shugaban kasar Mexico AP - Fernando Llano

Wannan karramawar ta zo ne makonni uku bayan zanga-zangar adawa da sake fasalin zabensa da majalisar dokokin kasar ta amince da shi.

Sauye-sauyen na barazana ga hukumar zabe ta kasa (INE) da ke da alhakin shirya zaben a cewar 'yan adawa da wani bangare na kungiyoyin fararen hula, wadanda suka sanar da daukaka kara zuwa kotun koli.

Wannan takun-saka tsakanin ‘yan adawar dai wani bangare ne na yakin neman zabe kafin zaben shugaban kasa na gaba da aka shirya gudanarwa a tsakiyar shekara ta 2024.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.