Isa ga babban shafi

Yan bindiga sun kashe mutane 12 a birnin Irapuato na kasar Mexico

Mutane 12 ne suka mutu kana wasu uku suka jikkata biyo bayan hari a ranar asabar  da aka kai a wata mashaya a birnin Irapuato da ke jihar Guanajuato da ke tsakiyar Mexico.

Taswirar kasar Mexico
Taswirar kasar Mexico AFP
Talla

Hukumomin  Irapuato sun tabbatar da mutuwar maza shida da mata shida, da kuma mutanen uku da suka jikkata, a cikin wata sanarwar manema labarai ba da cikakken bayani kan maharan ko kuma dalilin kai harin ba. Majiyoyin ‘yan sanda sun ce kisan ya faru ne da misalin karfe 7:51 na daren ranar Lahadi  lokacin da wasu gungun ‘yan bindiga suka shiga cikin ginin ta hanyar bude wuta kan mazauna wurin, kwastomomi da ma’aikata.

An tsinci gawar daya daga cikin wadanda abin ya shafa a kusa da wani babur, dab da mashayar, yayin da sauran gawarwakin aka same su a cikin gidan.

Karamar hukumar ta tabbatar da cewa ana ci gaba da gudanar da wani samame tare da goyon bayan ‘yan sanda, da sojoji, masu gabatar da kara da kuma jami’an tsaro na kasa domin gano wadanda suka yi kisan.

Harin ya zo ne kwanaki 11 kacal bayan wani zubar da jini da ya yi sanadin mutuwar mutane 20 a San Miguel Totolapan, wani gari a jihar Guerrero da ke kudancin kasar ta Mexico, sakamakon takaddamar da ta barke tsakanin kungiyoyin masu aikata laifuka.

Guanajuato, yanki mai bunkasuwar masana'antu, ya zama yanki mafi tashin hankali a Mexico, sakamakon fafatawa tsakanin kungiyoyin Santa Rosa de Lima da Jalisco Nueva Generación kan ayyukan da suke yi, da suka hada da safarar miyagun kwayoyi da satar mai.

A cewar hukumomin, a tsakanin watan Janairu zuwa Agusta, an kashe mutane 2,115 a wannan yanki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.