Harin 'yan bindiga a Mexico ya hallaka jami'an 'yan sandan kasar 13
Hukumomin Kasar Mexico sun ce wani harin 'yan bindiga ya kashe jami’an 'yan Sandan kasar guda 13 sakamakon kwantan baunar da aka musu a yankin Coatepec Harinas da ke Jihar Mexico.
Wallafawa ranar:
Rahotanni sun bayyana cewa daga cikin wadanda suka mutu sun hada da jami’an 'yan Sanda da kuma jami'an ofishin mai gabatar da kara na kasar.
Jihar Mexico na daya daga cikin yankunan da ke da hadarin rayuwa saboda ayyukan 'yan bindiga, kuma ya zuwa yanzu an kasha mutane sama da 300,000 tun bayan girke sojoji da gwamnati ta yi.
Tun a shekarar 2006 al'amuran tsaro suka sake tabarbarewa a Mexicon bayan tsanantar hare-haren 'yan bindigar da a lokuta da dama ke rutsawa da jami'an tsaro.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu