Isa ga babban shafi

Mexico ta kama kasurgumin dillalin muggan kwayoyi da FBI ke nema ruwa a jallo

Wata majiyar sojan ruwan kasar Mexico ta bayyana a cewa, an kama wani da ake zargi da laifin safarar miyagun kwayoyi a cikin jerin mutane 10 da hukumar FBI ta ke nema ruwa a jallo.

'Yan sanda Mexico
'Yan sanda Mexico AFP/Archivos
Talla

Rafael Caro Quintero, mai shekaru 69, Amurka na zarginsa da bada umarnin yin garkuwa da mutane da azabtarwa da kuma kisan wani jami'in hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi (DEA) Enrique "Kiki" Camarena a shekarar 1985.

Ya sha dauri a baya

Sai dai an kama shi a wancan lokacin, tare da yanke masa hukuncin daurin shekaru 40 a gidan yari saboda kisan Camarena, yayin da a shekarar  2013, wata kotu a Mexico ta ba da umarnin a saki Caro Quintero bayan ya kwashe shekaru 28 a kurkuku.

Sai kuma Kotun kolin Mexico ta soke hukuncin, amma Caro Quintero ya tsere a lokacin.

Dangantakar Mexico da Amurka

Lamarin ya jefa dangantakar Amurka da Mexico cikin rikici, kuma an dauki shekaru da dama kafin hukumomin yaki da fataucin miyagun kwayoyi a bangarorin biyu na kan iyaka su sake maido da dangantaka.

Caro Quintero, wanda ake yi wa lakabi da "Rafa," Hukumar FBI ta sanya tukaicin dala miliyan 20 ga duk wanda ya gano inda ya yake, bayan bayyana shi a matsayin "mai matukar hadari."

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.