Isa ga babban shafi
Mexico

Shahararren mai fataucin kwayoyi ya tsere daga gidan yarin Mexico

Shugaban Masu safarar miyagun kwayoyin kasar Mexico Joaquin Guzman da ake kira El Chapo, ya sake gudu daga gidanyarin da ake tsare da shi a karo na biyu. El Chapoya tsere daga gidan yarin ne, bayan ya tona rami a karkashin kasa a dakin dake da ake tsare da shi. 

Joaquin Guzman hannun 'yan sanda cikin shekarar data gabata
Joaquin Guzman hannun 'yan sanda cikin shekarar data gabata REUTERS/Edgard Garrido
Talla

Tuni hukumomin kasar suka baza jami’an tsaro don farautar El Chapo wanda ya tsere daga gidan yarin Altiplano dake da nisan kilomita 90 daga birnin Mexico City.

Shi dai El Chapo na da yara ko kuma abokan hulda kan safarar hodar ibilis a sassan duniya da dama, kuma an kama shi ne watanni 17 da suka gabata bayan ya kwashe shekaru 13 yana buya.

Kwamishinan tsaron Mexico Monte Alejandro Rubido yace, an gano cewar El Chapo yatsere ne lokacin da aka daina ganin sa a hotan kamarar da aka sanya a dakin sa, abinda ya sa aka bazama neman inda ya shiga.

‘Yan Sanda da sojoji 250 ke gadin gidan yarin na Altiplano.
Masu harkar safara miyagun kwayoyi sun dade suna cin Karen sub a babbaka a Mexico, yayin da hukumomin kasar ci gaba da kokarin shawo kan lamarin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.