Isa ga babban shafi
Mexico

Mutane 18 sun mutu a musayar wuta tsakanin masu safarar kwaya a Mexico

Musayar wuta da aka yi tsakanin gungu gungu na masu safarar miyagun kwayoyi ta yi sanadin mutuwar mutane 18 a Mexico, kamar yadda hukumomin kasar suka bayyana.

'Yan sandan Mexico a kan aiki.
'Yan sandan Mexico a kan aiki. REUTERS/Edgard Garrido
Talla

Lamarin ya auku ne a wani yanki na wajen gari, a arewa masu yammacin jihar Zacatecas, a cewar wata mai magana da yawun gwamnatin Rocio Aguilar.

Ta shaida wa wata kafar talabijin cewa an yi bata kashin ne tsakanin gungu gungu masu hamayya da juna, a kan mallakar yanki.

Garin Valparaiso ya yi iyaka da jihar Jalisco, wadda gida ne ga wani gungun masu safarar kwayoyi mai karfin gaske da ake kira Jalisco Nueva Generacion, kuma hukumomi sun sha alwashin kaddamar da yaki mai zafi a kansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.