Isa ga babban shafi
Amurka-Mexico

Amurka za ta bude iyakokinta na Mexico da Canada a watan gobe

Amurka ta sanar da shirin bude iyakokinta ta kasa ga matafiyan kasashen Mexico da Canada nan da farkon watan Nuwamba mai zuwa amma bisa sharadin tabbatar da duk wadanda za su ratsa hanyoyin sun karbi allurar rigakafin corona.

Wata iyakar Amurka da Mexico.
Wata iyakar Amurka da Mexico. PEDRO PARDO AFP
Talla

Tun daga watan Maris din 2020 ne Amurka ta kulle iyakokinta da kasashen na Canada da kuma Mexico makwabtanta don dakile yaduwar cutar wadda ta fantsama zuwa dukkanin kasashen Duniya a wancan lokaci.

Sai dai sanarwar ma’aikatar cikin gida na Amurkan, ta ce za ta bude iyakokin a farkon watan Nuwamba, duk da cewa ba ta fayyace hakikanin ranar da bude iyakokin za ta fara aiki ba.

Sanarwar ta nanata cewa dole ne sai matafiyan da suka karbi sahihiyar allurar rigakafin covid-19 sau biyu gabanin basu damar shiga cikin kasar ta Amurka.

Har zuwa yanzu dai mutanen da ba Amurkawa ba da suka ziyarci kasashen Birtaniya, China da kuma India baya ga Afrika ta kudu da Iran da kuma Brazil har ma da wasu kasashe na Turai basa samun damar shiga Amurka har sai sun killace kansu na tsawon kwanaki 14.

Tun cikin watan jiya ne gwamnatin Joe Biden ta sanar da shirin dage dokokin bayan samun nasarar yiwa kaso mai yawa na al’ummar kasar rigakafi da kuma samun raguwar masu kamuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.