Isa ga babban shafi
Amurka-Lafiya

Amurka ta sauya matsayinta kan maganin Aspirin

Kasar Amurka ta yi amai ta tande dangane da shawarar da ta bai wa mutanen da suka zarce shekaru 60 a duniya, cewar su rika shan maganin Aspirin kowacce rana domin kare su daga kamuwa da cutar bugun zuciya ko kuma shanyewar barin jiki.

Kwayar maganin Aspirin
Kwayar maganin Aspirin A. DE FREITAS
Talla

Masana kiwon lafiyar daga bangaren gwamnatin Amurka sun bai wa mutanen da suke tsakanin shekaru 40 zuwa 59 shawarar tintibar likitocinsu kafin yanke hukunci akan shan maganin domin kauce wa kamuwa da cutar bugun zuciya.

Wannan sanarwa ba karamar koma baya ba ce a bangaren kula da lafiyar Amurka, inda shan maganin Aspirin kowacce rana ya zama ruwan dare, saboda yadda yake rage kaurin jinin bil'adama da kuma hana daskarewar jini da kare mutane daga samun bugun zuciya ko shanyewar wani sashe na jiki.

Tun daga shekarar 2016, kwamitin kwararrun kula da lafiya na gwamnatin Amurka ya bada shawarar amfani da maganin na Aspirin ga mutanen da suka wuce shekaru 50 wadanda ke da kashi 10 ko sama da haka na hadarin samun bugun zuciya a cikin shekaru 10 masu zuwa.

Kwamitin a wancan lokaci ya ce, ga mutanen da suka wuce shekaru 60 kuma, su suke da damar yanke hukunci akan rayuwarsu.

Bincike daga baya ya kalubalanci wannan matsayi da shawarar da masanan suka gabatar.

Sai dai a ranar Talata, masanan sun ce, tasirin Aspirin ba zai iya kare mutane daga barazanar kamuwa da bugun zuciyar ko kuma shanyewar wani sashe na jiki ba.

Daya daga cikin masanan John Wong ya ce shan maganin Aspirin din kowacce rana na iya taimaka wa wasu mutane, amma kuma yana iya yin illar da ta shafi zubar jini a jikin bil'adama.

Wong ya ce yana da muhimmanci mutanen da ke tsakanin shekaru 40 zuwa 59, kuma ba su da tarihin cutar zuciya su tuntubi likitocinsu kafin shan maganin.

Sanarwar ta ce za a ci gaba da mahawara akan batun har zuwa farkon watan Nuwamba mai zuwa.

Akalla Amurkawa dubu 600 ke samun bugun zuciya, yayin da dubu 610 ke samun shanyewar wani sashe na jikin su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.