Isa ga babban shafi

Taimako daga Mexico, Venezuela ya isa Cuba me fama da mummunar gobara

Jiragen sama da ma'aikatan kashe gobara da kwararru daga Mexico da Venezuela sun isa Cuba, domin taimakawa wajen kashe wata gagarumar gobara a wani ma'ajiyar man fetur da ta yi sanadin mutuwar mutum daya, mutane 121 suka jikkata, yayin da wasu 17 suka bace.

kwararru, dauke da tan 20 na sinadaran kashe gobara sun isa yankin yanzu haka.
kwararru, dauke da tan 20 na sinadaran kashe gobara sun isa yankin yanzu haka. REUTERS - ALEXANDRE MENEGHINI
Talla

Tawagar agajin sun sauka a filin jirgin saman da ke gabar tekun Varadero mai tazarar kilomita 40 gabas da birnin Matanzas, inda tankunan mai guda biyu ke ci gaba da ci da wuta, tun bayan da wata walkiya ta tayar da gobarar a ranar Juma'a.

Jirgin Boeing 737-700 na Sojojin saman Mexico ya sauka tare da ma'aikatan ceto na soji 60 da masu fasaha 16 na Petroleos Mexicanos, yayin da kayan aiki da sinadarai na kashe gobara suka isa a jirgi na biyu.

Haka kuma wani jirgin na Conviasa ya isa yankin daga Venezuela tare da jami’an kashe gobara 35, da kuma wasu kwararru, dauke da tan 20 na sinadaran kashe gobara.

Guguwar da bakin hayaki na tashi a tashar jirgin ruwa da ke yankin masana'antu na Matanzas, wani birni mai tazarar kilomita 100 gabas da Havana.

Hukumomi sun ce an kwashe wasu mutane 1,900 daga yankin da lamarin ya shafa.

An sallami tamanin da biyar daga cikin wadanda suka jikkata yayin da 36 ke kwance a asibiti, biyar daga cikinsu na cikin mawuyacin hali, a cewar rahotannin likitoci na baya-bayan nan.

Daga cikin wadanda suka jikkata akwai ministan makamashi Livan Arronte.

Ofishin shugaban kasar ya ce jami'an kashe gobara 17 suka bata a halin yanzu.

Shugaban kasar Miguel Diaz-Canel ya nuna godiya ga gwamnatocin Mexico, Venezuela, Rasha, Nicaragua, Argentina da Chile saboda taimakon da suka bayar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.