Gobara ta halaka bakin-haure kusan 40 a Mexico
Bakin-haure kimanin 39 ne suka mutu sakamakon wata gobarar da ta tashi a wani gida da ake tsare bakin-hauren a Mexico, kusa da iyakarta da Amurka a Talatar nan.
Wallafawa ranar:
Hotunan da aka dauko daga inda lamarin ya faru sun nuno dimbim gawarwaki kwance a wasu shimfidu a wajen gidan da ke yankin Ciudad Juarez, ana kuma iya ganin motocin daukar marasa lafiya a kusa da su.
Wani jami’in cibiyar horarwa ta hukumar kula da shige da fice, wanda ya so a sakaya sunasa ya tabbatar da adadin wadanda suka mutu, kana ya ce mutane 29 ne suka jikkata.
Ciudad Juarez, wani mahimmmin yanki ne da bakin –haure ke amfani da shi wajen tsallakawa Amurka. Gidajen yankin cike suke da bakin-haure da ke jiran damammakin ketarawa, ko kuma wadanda suka nemi mafaka a Amurka, kuma suke tsammanin amincewa a kowane lokaci.
Rahotanni sun ce mahukuntan Mexico sun kaddamar da bincike a kan lamarin, kuma tuni masu binciken suka isa inda aka yi gobarar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu