Isa ga babban shafi
Mexico - Bakin haure

An ceto bakin haure 600 da ke tafiya cikin tireloli biyu a Mexico

Cibiyar Kula da Hijira ta kasar Mexico ta sanar ceto wasu bakin haure 600 da suka fito daga kasashe 12 yayin da suke  cikin manyan motocin guda biyu.

Wasu bakin haure dake kokarin zuwa Amurka daga Mexico 18/11/21.
Wasu bakin haure dake kokarin zuwa Amurka daga Mexico 18/11/21. CLAUDIO CRUZ AFP
Talla

A cikin wata sanarwa da cibiyar ta fitar ta ce an gano mata 145 da maza 455, ‘yan kasashen yankin tsakiyar  Amurka, da ‘yan Afirka da kuma Indiya, a jihar Veracruz da ke kudu maso gabashin kasar.

Mafi rinjaye sun fito ne daga Amurka ta tsakiya, inda  401 daga cikinsu daga kasar Guatemala, Cibiyar ta kara da cewa wasu da dama sun fito ne daga Honduras da Nicaragua yayin da jimillan 37 suka fito daga Bangladesh, 6 kuma daga Ghana, sai kuma mutum daya daga Indiya da Kamaru.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.