Isa ga babban shafi
MEXICO

Gawawakin da aka samu a Mexico na bakin haure ne

JAMI’AN Gwamnatin kasar Mexico, sun bayyana cewa gawawakin mutane 72 da aka samu jiya a wata gona, na bakin haure ne dake hanyar tafiya kasar Amurka.Daya daga cikin mutanen da ya tsira da ransa, ya shaidawa Yan Sanda cewar, sun fito ne daga kasar Ecuador, yayin da wasu daga cikinsu suka fito kasahsen El Salvador, Honduras da Brazil.Mutumin yace an harbe su ne, lokacin da suka ki aiki wa wata kungiyar masu hada hadar hodar ibilis.Kasar Mexico dai na fama da matsalar hada hadar safarar miyagun kwayoyi abinda Gwamnatin kasar ke yaki da shi, kuma ya zuwa yanzu karo tsakanin jami’an tsaro da masu hada hadar yayi sanadiyar mutuwar mutane 28,000. 

mutane 72 da aka samu jiya a wata gona
mutane 72 da aka samu jiya a wata gona Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.