Isa ga babban shafi

Isra'ila na shirin yiwa shirin tsagaita wuta zagon kasa

Isra’ila ta kai wasu munanan hare-hare ta sama a zirin Gaza a daidai lokacin da ake shirin ci gaba da tattaunawar sulhu tsakanin Isra'ila da Hamas a Masar a yau Lahadi a daidai loakacin da gidan talabijin kasar ya bayyana shirin ci gaba da tattauna batun tsagaita buda wuta a yankin.

Trẻ em Palestine bị thương do vụ ném bom của Israel được điều trị tại bệnh viện ở Rafah, phía nam Dải Gaza. Ảnh ngày 29/03/2024.
Trẻ em Palestine bị thương do vụ ném bom của Israel được điều trị tại bệnh viện ở Rafah, phía nam Dải Gaza. Ảnh ngày 29/03/2024. AP - Hatem Ali
Talla

Isra’Ila ta kai wannan sabon harin ne a yayin da aka shirya zaman tattauna batun janye barin wuta da Isra’Ila ke yi ba kakkautawa akan Palasdinawa.

Ana gwabza kazamin fada ne a yankin Falasdinawa da aka yi wa kawanya, a sassan da ke dauke da asibitoci da dama, a yakin da aka kwashe kusan watanni shida ana gwabzawa, sakamakon harin da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba.

A yayin da Isra'ila ke ci gaba da zafafa barin wuta, tare da da hana shigar da kayan agaji a cikin Gaza.

Akalla mutane biyar ne suka mutu, wasu da dama kuma suka jikkata, a cewar wani ma’aikacin kungiyar agaji ta Red Crescent, yayin da sojojin Isra’ila suka ce ba su san komai akan wannan lamari ba.

Shaidu sun shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa, ‘yan Gazan ne da ke sa ido kan jigilar kayayyaki da kuma sojojin Isra’ila da ke kusa da su ne suka yi ta harbe-harbe, kuma motocin dakon kaya sun afkawa mutane.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.