Isa ga babban shafi

Isra'ila ta kashe mutane 42 ciki har da Sojin Syria 36 a harin da ta kai Aleppo

Akalla mutane 42 suka mutu ciki har da Sojojin Syria 36 a harin da Isra’ila ta kai birnin Aleppo da sanyin safiyar yau Juma’a bayan da ta yi zargin cewa makami mai linzami na baya-bayan nan da Hezbollah ta harba kasar ta Yahudawa ya fito ne daga birnin.

Wani yanki na birnin Aleppo a Syria.
Wani yanki na birnin Aleppo a Syria. AP - Omar Sanadiki
Talla

Rahotanni sun ce cikin mutanen da suka mutu har da mayakan Hezbollah na Lebanon 6 yayinda wasu tarin fararen hula kuma suka jikkata.

Yaki ya barke tsakanin Hezbollah da Isra’ila ne bayan da kungiyar ta nuna goyon baya ga Falasdinawan da Isra’ilan ke ci gaba da kashewa a yankin Gaza kari kan mayakan Houthi na Yemen da suma ke mara baya ga mayakan Hamas.

Zuwa yanzu Falasdinawan da Isra’ila ta kashe sun kai dubu 32 da 552 baya ga jikkata wasu dubu 74 da 980 yayinda rushe kusan dukkanin gine-ginen Gaza ciki har da wuraren tarihi.

Ko a jiya Alhamis sai da al’ummar Jordan suka gudanar da wata zanga-zangar kin jinin Isra’ila tare da kiran kasar ta kawo karshen kwarkwaryar yarjejeniyar zaman lafiyar da ke tsakaninta da kasar ta Yahudawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.