Isa ga babban shafi

Saudiyya ta sanar da ganin jinjirin watan azumin Ramadan

Saudiyya ta tabbatar da ganin jinjirin watan Ramadan a yau Lahadi, don haka gobe za a tashi da azumi a kasar.

Membobin kwamitin ganin wata na Saudiyya zaune a yankin Tumai gabanin sanar da ganin wata.
Membobin kwamitin ganin wata na Saudiyya zaune a yankin Tumai gabanin sanar da ganin wata. © Haramain Sharifain
Talla

Cikin wata sanarwa jim kadan bayan ganin watan, kwamitin duban watan ya ce gobe Litinin zai kasance 1 ga watan Ramadan hijira 1445 a Saudiyya, wanda ya yi daidai da 11 ga watan Maris na shekarar 2024 miladiyya. 

Tuni hukumomin da ke kula da masallatan Haramin Makka da Madina suka bayyana kammaluwan shirye-shiryen fara gudanar da sallar Tarawihi a yau, sallar da a makon jiya mahukuntan kasar suka sanar da rage yawan raka'ao'in da ake yi daga 20 zuwa 10. 

Dangane da tsayuwar watan azumin, kasashe irinsu China, Oman sun sanar da rashin ganin jinjirin watan a yau, sabida haka su ka ce Talata ce za kasance 1 ga watan Ramadan a kasashensu. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.