Isa ga babban shafi

Isra’ila ta lalata masallatai sama da 1,000 a Gaza.

Tsawon kwanaki 107, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka dubu 25,105 da jikkata mutum dubu 62,681.

Wani daga cikin Masalltan da hare-haren Isra'ila suka lalata a yankin Gaza.
Wani daga cikin Masalltan da hare-haren Isra'ila suka lalata a yankin Gaza. REUTERS - STRINGER
Talla

Ma'aikatar addini ta Gaza ta ce ana bukatar kusan dala miliyan 500 domin sake gina wadannan masallatai.

Isra’ila ta lalata masallatai sama da dubu 1,000 a Gaza tun daga ranar 7 ga watan Oktoba, kamar yadda hukumomi suka tabbatar.

 

“Sake gina wadannan masallatan zai ci kudi kimanin dala miliyan 500,” kamar yadda Ma’aikatar Harkokin Addini da ke Gaza ta bayyana a wata sanarwa.

Akwai kimanin masallatai 1,200 a Zirin Gaza. Ma’aikatar ta ce Isra’ila ta kashe malamai masu wa’azi sama da 100 tun bayan soma wannan yakin.

 

Wani sojan Isra’ila wanda bai jima da dawowa daga yaki a Gaza ba ya kashe abokinsa a Tel Aviv, yayin da ya bishi har gida ya kuma bindige shi, kamar yadda kafafen yada labarai na Isra’ila suka bayyana.

Kafafen watsa labaran Isra’ila a cikin ‘yan kwanakin nan sun ruwaito cewa akwai dubban sojoji wadanda suka je yaki Gaza suka dawo da ke fuskantar matsalar kwakwalwa.

Isra'ila na ci gaba da yin luguden wuta kan gidajen Falasdinawa musamman a Gaza.  

Isra'ila ta kashe karin Falasinawa 178 da kuma raunata 293 a cikin sa'o'i 24 da suka gabata, kamar yadda Ma'aikatar Lafiya da ke Gaza ta tabbatar.

Ko a jiya Asabar sai dai ma'aikatar ta ce sojojin na Isra'ila sun kashe mutum 165 tsakanin Juma'a zuwa Asabar.

Zuwa yanzu dai Isra'ila ta kashe Falasdinawa dubu 25,105 da kuma raunata wasu dubu 62, 681 tun daga 7 ga watan Oktoba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.