Adadin wadanda suka mutu a hare-haren Isra'ila a Gaza ya kusan dubu 25 - Hamas
A yayin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare hare yankin Zirin Gaza a kokarin da take na kakkabe mayakan Hamas, ma’aikatar lafiyar yankin ta ce adadin wadanda suka mutu ya zuwa yanzu ya tasam ma dubu 25.
Wallafawa ranar:
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Fira ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, wanda ke shan caccaka daga cikin kasarsa ya yi watsi da kiran samar da kasar Falasdinu bayan wannan yaki.
Ma’aikatar lafiyar Gaza ta ce akalla mutane 165 ne suka mutu sakamakon hare-haren Israila a cikin sa’o’i 24, adadin da ya ninka wanda aka samu a ranar Juma’a.
Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ruwaito cewa an yi ta jin kararrakin harbe-harbe da fashe-fashe a kudancin Zirin Gaza, musamman a birnin Khan Younis.
Tun bayan harin da mayakan Hamas suka kai Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2023 ne fada ya barke tskanin kasar ta Yahudu da mayakan Hamas, wadda ta sha alwashin kakkabe mayakan, lamarin da ya sa ta ke ta kai hare-hare ba kakkautawa a yankin Zirin Gaza.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu