Isa ga babban shafi

Isra'ila ta yi luguden wuta a kan wani asibitin kudancin Gaza

Kungiyar agaji ta Red Crescent ta zargi Isra’ila da kai hari da jirgi mara matuki a kan wani asibiti a birnin Khan Younis, a Juma’a, a daidai lokacin da hare-haren da ta ke ci gaba da kai wa kudancin Zirin Gaza ke barazana ga cibiyoyin lafiyar da ke aiki har yanzu a yankin da rikicin ya daidaita.

Hayaki kenan da ya turnike sararin samaniyar birnin Khan Younis sakamakon hare-haren Isra'ila.
Hayaki kenan da ya turnike sararin samaniyar birnin Khan Younis sakamakon hare-haren Isra'ila. AP - Mohammed Dahman
Talla

Mutane da dama ne suka ji rauni sakamakon luguden wutar da jirage mara matuki na Israila suka kai asibitin Al-Amal da ma shelkwatar kungiyar agajin.

 

Rundunar sojin Isra’ila ta ce tana nazari a kan wannan rahoto. 

 

A kusa da wurin da aka kai harin jirgi mara matuki, rahotanni sun ce an hango tankuna yakin Isra’ila suna wucewa ta kusa da asibiti mafi girma da ya rage a yankin, wato Nasser, inda aka yi ta jink kararrakin harbe harbe da fashe-fashe, kana ganau suka ce an yi bata -kashi.

Isra’ila takadamar da wani gagarumin hari a kan Khan Younis a wannan  makon da zummar kame birnin, wanda  ta ce  yanzu ya zama sheljwatar mayakan Hamas, wadanda suka kai mata hari a ranar 7 ga watan Oktoba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.