Isa ga babban shafi

Dakarun Isra'ila sun gano gawar matashi Elia da Hamas ta yi garkuwa da shi a Gaza

Dakarun Isra’ila sun gano gawar matashi Elia Toledano mai shekaru 28 dan asalin Faransa da Isra’ila bayan da dakarun Hamas suka yi garkuwa da shi.

Yakin ya kuma rinchabewa da safiyar yau
Yakin ya kuma rinchabewa da safiyar yau AFP - -
Talla

Hamas ta yi garkuwa da Teledano a wajen wasan wake-wake da kade-kade da ya halarta ranar 7 ga watan Octoban da ya gabata.

Kisan wannan matashi ya kara sanya Isra’ila zafafa hare-haren ta da safiyar nan, bayan samun cikakken goyon baya daga Amurka wadda ke ganin Isra’ila na daukar fansa ne kan harin da Hamas ta kai mata watanni biyu da suka gabata.

A yanzu dai yakin ya lakume rayukan fararen hula fiye da dubu 18 yayin da Isra’ila ta ce sojojin ta fye da 100 sun mutu a sanadin yakin, duk da dai sune suka kashe juna bisa kuskure.

Har yanzu babu wani cikakken bayani game da yawan mayakan Hamas da suka mutu a sanadin yakin, sai dai kuma bayanai na cewa Isra’ila na ci gaba da cika ramukan da suke samun mafaka da nufin tilasta musu fitowa don fafata yakin gaba da gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.