Isa ga babban shafi

Iraki ta janye jakadanta na Iran kan harin makami mai linzami a kan yankin Kurdawa

Iraqi ta yi wa jakadanta kiran gaggawa daga Tehran bayan wasu hare-haren makamai masu linzami da Iran ta kai kan yankin Kurdawa mai kwarya-kwaryar ‘yanci dai dai lokacin da rikici ke ci gaba da tsananta a yankin gabas ta tsakiya. 

 Nuri al-Maliki Fira ministan Iraqi.
Nuri al-Maliki Fira ministan Iraqi. Reuters
Talla

 

Iraqi ta matukar fusata da harin na Iran wanda Tehran ta yi ikirarin cewa ta kai ne kan ofishin leken asirin Isra’ila da ke yankin na Kurdawa wanda ya kashe mutane 4 a matsayin fansar kisan kwamandojinta da Isra’ilan ta yi. 

A cewar Iraqi za ta mika batun gaban kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya dangane da harin na Iran wanda kuma ya shafi wani yanki na yammacin Baghdad da ke makwabtaka da Syria wajen da dandazon mayakan IS ke girke. 

Tuni dai harin wanda ya kasha mutane 4 tare da jikkata wasu 6 ya gamu da kakkausar suka daga Amurka wadda alakarta da Iran ke ci gaba da tsami kasancewar kasar mai goya baya ga mayakan Hamas. 

Iran ta kare hare-haren nata a Iraqi da Syria da cewa martani ne da hukunci kan duk wadanda ke da hannu wajen kalubalantar tsaron kasar. 

Dakarun juyin juya halin Iran sun ce harin na su ya yi nasarar lalata shalkwatar leken asirin Syria da ke yankin na Kurdawa. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.