Isa ga babban shafi

Hamas ta saki karin mutanen da ta ke garkuwa da su bayan jinkirin sa'o'i

Kungiyar Hamas ta yankin Falasdinu ta saki karin wasu daga cikin mutanen da take garkuwa da su a bayan da aka samu jinkiri na kusan sa’o’i 7, abin da ke nuni da cewa kwarya-kwaryar yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki 4 da ta cimma da Isra’ilar ta ci gaba da aiki.

Daya daga cikin fursunoni  Falasdinawa da Isra'ila ta saki.
Daya daga cikin fursunoni Falasdinawa da Isra'ila ta saki. AP - Mahmoud Illean
Talla

An samu jinkirin ne bayan da  kungiyar Hamas ta  zargi Isra’ila da rashin mutunta nata bangare na yarjejeniyar, lamarin da ya sa Hamas ta nemi dole sai ta  bari an shigar da kayayyakin agaji yankin Zirin Gaza kafin ta ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar.

Amma an samu masalaha ta wajen warware matsalar da ta  janyo jinkirin, bayan da kasashen Qatar da Masar suka shiga Tsakani.

Bayan wannan shiga tsakanin ne Hamas ta amince ta ci gaba da sakin wasu mutane 17 daga cikin wadanda ta ke garkuwa  da su kamar yadda ya ke a cikin yarjejeniyar, a yayin da a nata  bangaren, Isra’ila ta  saki fursunoni Falasdinawa 39.

Daga cikin wadanda Hamas ta saki, akwai Isra’ilawa 13 da wasu mutane 4 ‘yan kasar Thailand, kuma ta mika  su ne da kungiyar agaji ta Red Cross a cikin talatainin daren Asabar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.