Hamas za ta ci gaba da sakin wadanda ta ke garkuwa da su
Hamas za ta ci gaba da aiki da yarjejeniyar sakin wadanda take garkuwa da su a daren Asabar din nan bayan da aka warware matsalar da ta taso a game da shigo da kayan agaji arewacin Gaza, sakamakon shiga tsakani da Masar da Qatar suka yi.
Wallafawa ranar:
Wani jami’in Falasdinu da ke da masaniya a game da yunkurin diflomasiyar ya ce Hamas za ta ci gaba da mutunta kwarya-kwaryar yarjejeniyar ta kwanaki hudu kamar yadda ta kulla da Isra’ila, tsagaaita wuta ta farko da aka cima tun da aka fara wannan rikici a ranar 7 ga watan Oktoba.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajenn Qatar, Majed Al Ansari ne ya tabbatar da warware wannan matsalar da ta taso daga baya a dandalin sada zumunta, inda ya ce a cikin wannan dare Hamas za ta saki Yahudawa 13 da wasu ‘yan kasashen waje 7, a yayin da Isra’ila za ta sakar mata Falasdinawa 39.
Tun da farko, Jagorancin mayakan Hamas ta ce za a jinkirta sakin wadanda take garkuwa da su idan Isra’ila ba ta yi biyayya da ilahirin yarjeniyoyin da aka cimma a game da sakin Falasdinawan da take tsare da su a gidajen yarinta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu