Hamas ta jinkirta sakin wadanda take garkuwa da su
Kungiyar Hamas ta yanke shawarar jinkirta sakin rukuni na biyu na wadanda ta ke garkuwa da su a Asabar din nan kamar yadda aka tsara, har sai Isra’ila ta cika alkawarinta na barin manyan motoci dauke da kayayyakin agaji su shiga Gaza.
Wallafawa ranar:
Jagorancin mayakan Hamas ta ce za a jinkirta sakin wadanda ake garuwa da su idan Isra’ila ba ta yi biyayya da ilahirin yarjeniyoyin da aka cimma a game da sakin Falasdinawan da take tsare da su a gidajen yarinta.
Babu wani martini daga Isra’ila a game da wannan mataki na Hamas.
Tun da farko wani kakakin sojin Isra’ila ya ce idan har babu wani abin da ya sauya, ana sa ran sakin mutane 13 daga cikin wadanda Hamas ta yi garkuwa da su a Asabar din nan. Ya ce Isra’ila za ta saki fursunoni Falasdinawa 39.
A karkashin wannan yarjejeniya da aka kulla tsakanin Hamas da Isra’ila, za a yi musayar jimillar mutane 50 wadanda aka yi garkuwa da su da Falasdinawa 150 da ke gidajen yarin Isra’ila a cikin kwanaki 4.
Wannan koma-baya da aka samu a Asabar dinnan na zuwa ne ‘yan sa’o’i bayan da Masar, wadda ke da iko da mashigin Rafah na Kudancin Gaza ta ce ta ga alamar cewa akwai yiwuwar tsawaita kwarya-kwaryar tsagaita wutar da aka cimma tsakanin bangarorin biyu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu