Isa ga babban shafi

An soma taron jin kai kan Gaza a birnin Paris na kasar Faransa

Faransa ta karbi bakuncin taron jin kai kan Gaza,wanda ba a taba ganin irinsa ba tun bayan harin da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba.A wannan taro na Paris da aka shirya a fadar Elysée gwamnatin Isra'ila ba ta aike da wakili ba ,sai dai majiya daga fadar Shugaban na Faransa na cewa shugaba Macron  ya tattauna da Firaminista Benjamin Netanyahu farkon wannan mako.

O presidente francês Emmanuel Macron fala ao lado de representantes de estados, organizações internacionais, empresas, bancos de desenvolvimento e ONGs durante uma conferência humanitária internacional para civis em Gaza, no Palácio Presidencial do Eliseu, em Paris, França, em 9 de novembro de 2023.
O presidente francês Emmanuel Macron fala ao lado de representantes de estados, organizações internacionais, empresas, bancos de desenvolvimento e ONGs durante uma conferência humanitária internacional para civis em Gaza, no Palácio Presidencial do Eliseu, em Paris, França, em 9 de novembro de 2023. via REUTERS - POOL
Talla

Kazzalika Shugaba Macron ya kuma tattauna ta wayar tarho da shugaban Masar Abdel Fattah al-Sissi da Sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamad Al-Thani, wanda kasashensu ke taka muhimmiyar rawa wajen inganta isar da kayan agaji a zirin Gaza, inda Falasdinawa miliyan 2.4 ke fuskantar karancin abinci da ruwan sha.

Rashin kasancewar Isra’ila bai hana hukumar Falasdinu ta aike da Firaministanta  da ya jagoranci tawagar da suka bi ta hanyar mashigin Gaza a wannan lokaci da Masar, wacce ke ikon mashigar Gaza daya tilo da Isra'ila ba shi hannun Isra’ila.

Le président français Emmanuel Macron s'exprime aux côtés de représentants d'États, d'organisations internationales, d'entreprises, de banques de développement et d'ONG lors d'une conférence humanitaire internationale pour les civils de Gaza, au palais présidentiel de l'Élysée, à Paris, le 9 novembre 2023.
Le président français Emmanuel Macron s'exprime aux côtés de représentants d'États, d'organisations internationales, d'entreprises, de banques de développement et d'ONG lors d'une conférence humanitaire internationale pour les civils de Gaza, au palais présidentiel de l'Élysée, à Paris, le 9 novembre 2023. AFP - LUDOVIC MARIN

Wani bincike na nuni cewa kungiyoyin agaji na bin diddigin taron, inda suka yi Allah-wadai da rashin samar da kayan agaji, a dai-dai lokaci da Faransa ta sanar da ware kudi milyan 100 na Yuro a matsayin tallafi.

Kungiyoyi masu zaman kansu 13 sun yi kira da a tsagaita bude wuta cikin gaggawa, suna neman "tabbatar da shigar da kayan agaji a Gaza da mutunta dokokin jin kai na kasa da kasa".

Distribution de nourriture à Rafah, dans le sud de la bande de Gaza, le 8 novembre 2023.
Distribution de nourriture à Rafah, dans le sud de la bande de Gaza, le 8 novembre 2023. AP - Hatem Ali

Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta bukatar agaji ga al'ummar Gaza da gabar yammacin kogin Jordan akan dala biliyan 1.2 har zuwa karshen shekarar 2023.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.