Isa ga babban shafi

Babban jami'in diflomasiyyar Iran ya gana da yariman Saudiyya

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya gana da yarima mai jiran gado na Saudiyya a ranar Juma'a a ziyararsa ta farko tun bayan da kasashen biyu da ke adawa da juna a Gabas ta Tsakiya suka sanar da sasantawa da juna na ba-zata.

Ministan harkokin wajen kasar Iran Hossein Amir-Abdollahian kenan daga hagu tare da Yariman Saudiyya Muhammad Bin Salman
Ministan harkokin wajen kasar Iran Hossein Amir-Abdollahian kenan daga hagu tare da Yariman Saudiyya Muhammad Bin Salman © reuters
Talla

Hossein Amir-Abdollahian, wanda ya tafi Riyadh a ranar Alhamis, ya tattauna da Mohammed bin Salman a Jeddah, kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen Saudiyya ta sanar, bayan tsawaita ziyarar kwana guda da aka tsara.

a cewar sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen kasar ta wallafa a shafin X, wanda aka fi sani da Twitter, ta ce kasashen biyu sun yi nazari kan alakar da ke tsakanin su, da kuma damar samun hadin gwiwa a nan gaba, da hanyoyin bunkasa alakarsu, baya ga tattauna ci gaban da ake samu a fagen shiyya-shiyya da na kasa da kasa.

Kamfanin dillancin labaran IRNA, ya ya ce, ziyarar ita ce karo ta farko da wani babban jami’in gwamnatin Iran ya gana da yarima Mohammed mai shekaru 37, wanda ya kawo wasu sauye-sauye a masarautar ta saudiyya.

Amir-Abdollahian ya kira taron na tsawon mintuna 90, a matsayin samar da ci gaba da inganta alakar kasashen biyu da kuma tsaro.

Iran mai rinjayen mabiya mazhabar Shi'a da Saudiyya mai mulkin 'yan Sunni sun yanke huldar dake tsakaninsu a shekarar 2016, amma kuma sun amince da maido da huldar diflomasiyya a wata yarjejeniya da China ta kulla a watan Maris.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.