Isa ga babban shafi

China ta taka muhimmiyar rawa wajen gyara alakar Iran da Saudiya

Shugaba Xi Jinping na China ya taka gagarumar rawa wajen sasanta rikicin da ke tsakanin Saudi Arabia da Iran don ganin manyan kasashen biyu sun dinke barakar da kuma kulla sabuwar huldar dangantaka. 

Babban jami'in diflomasiyyar China Wang Yi tare da wakilcin kasashen Iran da Saudi Arabia a wajen kulla yarjejeniyar dawowar hulda tsakanin kasashen biyu.
Babban jami'in diflomasiyyar China Wang Yi tare da wakilcin kasashen Iran da Saudi Arabia a wajen kulla yarjejeniyar dawowar hulda tsakanin kasashen biyu. via REUTERS - CHINA DAILY
Talla

Wani jami’an gwamnatin Saudi Arabia ya tabbatarwa kamfanin dillancin labaran Faransa cewar wannan ne dalilin da ya sa kasashen biyu suka sanar da gudanar da tarurruka a tsakaninsu da zummar dawo da dangantaka a makon jiya. 

Jami’in ya ce tun a watan Disambar bara lokacin da Saudiya ta karbi bakuncin shugaban China aka tattauna batun kulla sabuwar huldar tsakanin Iran da Saudi Arabia, yayin tattaunawa tsakanin shugaba Xi da Yarima Muhammad bin Salman. 

A lokacin shugaban na China ya bayyana aniyarsa ta ganin kasarsa ta shiga tsakanin kasashen biyu domin tattauna matsalolin da ke tsakaninsu da kuma sasantawa da juna, batun da Yarima Salman ya amince da shi. 

Jami’in ya ce ganin muhimmancin China ga Iran, wadda ita ce ta biyu wajen hulda da kasar, nan-da-nan ta amince da tayin, abinda ya kai ga tattaunawa daban daban kafin sanarwar da akayi a makon jiya. 

Wadannan ganawar da kasashen biyu suka yi sun hada da wadda aka yi tsakanin ministocin harkokin wajen kasashen Saudi Arabia da Iran a Jordan a watan Disamba da ganawar da aka  yi tsakanin mataimakin ministan harkokin wajen Saudiya da na Iran lokacin rantsar da shugaban kasar Brazil Inacio Lula da Silva a watan Janairu da kuma ziyarar shugaba Ebrahim Rais na Iran zuwa Bejing a watan Fabarairu. 

Ana fatar wannan sabon yunkuri ya kawo karshen katse huldar danganta ta shekaru 7 da kasashen biyu suka yi, tare da mutunta muradun kowacce kasa a tsakaninsu da kuma kaucewa katsalandan a harkokin cikin gidan kowacce kasa. 

Ya zuwa yanzu dai Amurka wadda ta ke hulda ta kut-da-kut da Saudi Arabia baya ga takun saka da Iran ba ta ce komai a hukunce dangane da wannan sabon yunkuri ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.