Isa ga babban shafi

Sama da yara dubu 11 ne aka kashe ko nakasar a yakin Yemen- UNICEF

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya ce Sama da kananan yara 11,000 ne aka kashe ko suka nakasa tun bayan barkewar yakin basasa a kasar Yemen kusan shekaru takwas da suka gabata.

Wani yaro da ya jikkata a wani hari da jiragen yakin rundunar kawancen da Saudiyya ke jagoranta suka kai, yana kwance a wani asibiti da ke Saana na kasar Yemen.
Wani yaro da ya jikkata a wani hari da jiragen yakin rundunar kawancen da Saudiyya ke jagoranta suka kai, yana kwance a wani asibiti da ke Saana na kasar Yemen. AP - Hani Mohammed
Talla

Shugabar asusun kula da kananan yara ta UNICEF Catherine Russell  tace "Dubban yara ne suka rasa rayukansu, wasu dubbai kuma suna cikin hadarin mutuwa saboda cututtuka da za a iya rigakafin su.

Russell wadda ta kammala ziyara a kasar kwannan nan ta yi kira ga gwamnati da ‘yan tawayen Houthi su sabanta yarjejeniyar tsagaita wuta da suka cimma.

Yarjejeniyar da aka kulla tun da farko a wataan Afrilu, ta taimaka wajen rage zafin rikicin.

Sai dai tun bayan da yarjejeniyar ta daina aiki, rahotanni sun ce yara 62 aka kashe  a tsakanin farkon watan Oktoba  da 30 gaa watann Nuwamba.

Bugu da kari, akalla yara 74 na daga cikin mutane 164 da suka samu rauni ko kuma suka mutu sakamakon taka nakiya a tsakanin wataannin Yuli da Satumba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.