Isa ga babban shafi

An binne 'yar jarida Shireen Abu Akleh

An binne fitacciyar 'yar jaridar gidan talabijin din Aljazeera Shireen Abu Akleh a wata makabarta da ke gabashin birnin Kudus, kwanaki uku bayan da jami'an tsaron Isra'ila suka harbe ta har lahira, a lokacin da take daukar rahoto kan wani samame da jami’an tsaron suka kai a kusa da sansanin 'yan gudun hijira da ke yankin Jenin a gabar yamma da  kogin Jordan.

Dubban Falasdinawan da suka halarci taron jana'izar binne fitacciyar 'yar jaridar kafar watsa labaran Aljazeera Shireen Abu Akleh a birnin Kudus.
Dubban Falasdinawan da suka halarci taron jana'izar binne fitacciyar 'yar jaridar kafar watsa labaran Aljazeera Shireen Abu Akleh a birnin Kudus. © Ammar Awad, Reuters
Talla

Dubban mutane ne suka taru don jana'izar binne Shireen Abu Akleh a jiya Juma'a, wadanda suka hada da dangi, abokai, da wadanda suka santa  a matsayin fitacciyar mai daukarwa Al Jazeera rahotanni kan yankunan Falasdinawa da Isra’ila ta mamaye da kuma lamurran rayuwar Falasdinawa na yau da kullum.

Hoton marigayiya Shireen Abu Akleh.
Hoton marigayiya Shireen Abu Akleh. REUTERS - IMAD CREIDI

Tuni Amurka, da Tarayyar Turai da Majalisar Dinkin Duniya suka goyi bayan gudanar da cikakken bincike kan abin da Al Jazeera ta yi wa lakabi da kisan gilla da gangan, sai dai Hukumar yankin Falasdinu ta ki amincewa da gudanar da binciken na hadin gwiwa da Isra'ila.

Da fari dai Fira Ministan Isra'ila Naftali Bennett ya ce mai yiwuwa mayakan Falasdinu ne suka kashe ‘yar jaridar bisa kuskure, sai dai daga bisani ministan tsaro Benny Gantz ya amince da cewa watakila jami’an tsaronsu ne suka harbe ta ko kuma Falasdinawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.