Isa ga babban shafi
Masallacin Kudus

Erdogan ya nuna bacin ransa kan harin Masallacin Kudus

Shugaban Kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana matukar bacin ransa da tashin hankalin da ake samu a Masallachin Al Aqsa dake Birnin Kudus, lokacin da ya tattauna ta waya da shugaban Israila Isaac Herzog.

Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan
Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan AP - Ebrahim Noroozi
Talla

Kalaman Erdogan na zuwa ne bayan arangamar da aka samu tsakanin Yahudawa da Falasdinawa a ciki da wajen Masallachin, wanda ya kaiga raunata mutane sama da 170 akasarin su Falasdinawar dake zanga zanga saboda matakan da jami’an tsaron Israila ke dauka.

Wannan tashin hankalin na zuwa ne kusan shekara guda da irin sa da aka gani wanda aka kwashe kwanaki 11 ana fafatawa tsakanin Israila da Falasdinawa masu tsatsauran ra’ayi dake Gaza.

Masallachin Al Aqsa na da matukar muhimmanci ga mabiya addinin Yahudawa, yayin da kuma shine wurin ibada mafi kima ga Musulmi bayan Masallachin Makkah da na Madinah.

Tashin hankalin da aka samu a karshen mako ya sanya Israila amfani da karfi wajen kai harin sama Yankin Gaza da kuma tura sojojin ta domin farautar masu tsatsauran ra’ayi a Yankunan Falasdinawa.

Erdogan yace hotunan da suke gani na yadda ake kaiwa Falasdinawa hare hare a Masallachin abin Allah wadai ne, wanda ke iya samun martani daga kasashen Musulmin duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.