Isa ga babban shafi

Falasdinawa sun karrama 'yar jarida Shireen Abu Akleh

Dubban Falasdinawa a wannan Alhamis sun karrama 'yar jaridar Al Jazeera Shireen Abu Akleh a gabar yammacin kogin Jordan, kwana guda bayan da aka harbe ta yayin wani samame da sojojin Isra'ila suka kai.

Dakarun musamman na yankin Falasdinu dauke da gawar 'yar jaridar kafar watsa labarai ta Aljazeera Shireen Abu Akleh.
Dakarun musamman na yankin Falasdinu dauke da gawar 'yar jaridar kafar watsa labarai ta Aljazeera Shireen Abu Akleh. AFP - ABBAS MOMANI
Talla

Isra'ila da Falasdinawa dai sun yi ta tuhumar juna kan kisan ‘yar jaridar da ta kasance Bafalasdiniya kuma Ba'amurkiya mai shekaru 51 da haihuwa, jigo a sashin Larabci na fitacciyar kafar watsa Labarai ta Aljazeera da ke kasar Qatar, wadda ta rasa ranta a yayin da take tsaka da daukar rahoton arrangamar da ake yi a sansanin 'yan gudun hijira na Jenin.

Amurka, da Tarayyar Turai da Majalisar Dinkin Duniya duka sun goyi bayan gudanar da cikakken bincike kan abin da Al Jazeera ta yi wa lakabi da kisan gilla da gangan, sai dai Hukumar yankin Falasdinu ta ki amincewa da gudanar da binciken na hadin gwiwa da Isra'ila.

Gawar Shireen Abu Akleh
Gawar Shireen Abu Akleh AP - Nasser Nasser

Saboda irin matsayin da marigayiya Shireen Abu Akleh ta samu a tsakanin Falasdinawa ne aka yi katafaren taron yi mata jana’iza a fadar shugaban yankin Falasdinu Mahmud Abbas, taron da ya samu halartar manyan jami'an diflomasiyya na kasashen waje, yayin da dubban mutane suka yi dafifi a kan tituna, domin yi tozali da akwatin gawarta da aka lullube da tutar Falasdinu, da aka ratsa ta tsakiyar birnin Ramalla da shi.

Yayin jawabin da ya gabatar a yau, shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas ya jaddada dora alhakin mutuwar marigayiya Shireen akan Isra'ila tare da yin watsi da batun gudanar da binciken hadin gwiwa da gwamnarin Isra’ilan.

Da fari dai Fira Ministan Isra'ila Naftali Bennett ya ce mai yiwuwa mayakan Falasdinu ne suka kashe ‘yar jaridar bisa kuskure, sai dai daga bisani ministan tsaro Benny Gantz ya amince da cewa watakila jami’an tsaronsu ne suka harbe ta ko kuma Falasdinawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.