Isa ga babban shafi
Iran - Isra'ila

Iran ta dauki alhakin harba makamai masu linzami cikin Iraqi

Kasar Iran ta dauki alhakin harba makamai masu linzami kan birnin Irbil da ke arewacin kasar Iraqi, wadanda ta ce ta yi nufin su afkawa wata cibiyar kasar Isra’ila ne.

Wani makami mai linzami na kasar Iran.
Wani makami mai linzami na kasar Iran. AFP/Getty Images - AFP
Talla

Kafin sanarwar ta Iran dai,  hukumar lardin Kurdistan da ke Iraqi ta ce makamai masu linzami 12 ne aka harba kan birnin na Irbil, wadanda suka jikkata fararen hula biyu da kuma rusa wasu gine-gine.

Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun tabbatar da harba makaman, suna masu ikirarin kai hari kan wuraren da Isra'ila ke amfani da su.

An dai sha kai hari kan kadarorin Amurka da kuma dakarun hadin gwiwa da rokoki da kuma jirage marasa matuka a kasar Iraqi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.