Isa ga babban shafi
Afghanistan - Taliban

Taliban ta haramta yi wa mata auren dole a Afghanistan

Kungiyar Taliban ta kafa dokar haramta yi wa mata auren dole a Afghanistan, tana mai cewa bai kamata a dauki matan a matsayin kadara ba, dan haka dole ne su amince da zabin wanda ake shirin aura musu.

Wasu mata a Kaboul babban birnin kasar Afghanistan.
Wasu mata a Kaboul babban birnin kasar Afghanistan. AP - Mariam Zuhaib
Talla

Shugaban kungiyar Taliban Hibatullah Akhunzada, da ake kyautata zaton yana kudancin birnin Kandahar ne ya sanar da kafa dokar hana auren dolen a jiya Juma’a.

Dokar dai ba ta ambaci adadin shekarun da za a yi wa mace aure ba, shekarun da a baya aka sanya na faraway daga 16.

Kungiyar ta Taliban ta kuma ce daga yanzu za a bar matar da mijinta ya rasu ta sake yin aure makwanni 17 bayan mutuwar mijinta, zalika da kanta za ta zabi sabon mijin da take son aura.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.