Isa ga babban shafi
Taliban-Rasha

Sai Taliban ta kare hakkokin dan adam za ta samu goyon bayan Duniya- Rasha

Fadar Kremlin ta gwamnatin Rasha ta bukaci Taliban ta tafiyar da mulkinta bisa kula da dokokin kare hakkin dan adam matukar kungiyar na fatan samun goyon bayan kasashen Duniya.

Wakilan Taliban yayin taron Rasha kan Afghanistan da ya samu wakilcin China da Pakistan.
Wakilan Taliban yayin taron Rasha kan Afghanistan da ya samu wakilcin China da Pakistan. Alexander Zemlianichenko POOL/AFP
Talla

Yayin wata tattaunawa tsakanin wakilan Taliban da ke ziyara a Moscow da mukarraban gwamnatin kasar, Kremlin ta bukaci kungiyar ta yi taka-tsan-tsan da dokokin hakkin dan adam tare da shigar da kowanne bangare tsarin tafiyar da gwamnati.

Manzon Rasha a Afghanistan, Zamir Kabulov ya ce Taliban ta amince da aikewa da wakilai Moscow don shiga tattaunawar wadda ta kunshi wakilai daga China da Pakistan, matakin da ya ce manuniya ce ta cewa kungiyar na da fatan shugabanci na kwarai a kasar.

Wakilcin na Taliban ya tabbatarwa Rasha kokarin da shugabancinsu ke yi na kiyaye dokokin kare hakkin dan adam tare da gudanar da mulki bisa tanadin doka.

Acewar wakilin na Rash aga Taliban, akwai bukatar shigar kasashen Duniya wajen ceto Afghanistan daga rushewa saboda matsalolin tattalin arziki da tsananin bukatar daukin da kasar ke yi ta fuskar abinci da magunguna saboda karancinsu.

Wakilin na Kremlin Kabulov y ace babu kasar da ke farin ciki da rsuhewar karbabbiyar gwamnatin Ashraf Ghani amma idan har duniya ta juye baya ga Afghanistan don tana fushi da Taliban kai tsaye al’ummar kasar ce za ta tagayyara ba kungiyar ba.

Taron na Moscow da ya samu halartar wakilcin kasashe 10 ya sha alwashin kada kuri’ar bukatar tattara kudin tallafi ga Afghanistan yayin zaman Majalisar Dinkin Duniya.

Sai dai mataimakin Firaministan Afghanistan Abdul Salam Hanafi ya ce ba wai taimakon Soji Kabul ke bukata ba, kawai goyon bayan tabbatar da zaman lafiya ta ke nema don fara aikin gyaran kasar wadda ke gab da rushewa.  

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.