Isa ga babban shafi
Taliban-Mata

Taliban na duba yiwuwar baiwa Mata damar karatu da aiki a Afghanistan

Taliban ta sanar da shirin baiwa mata damar komawa makarantu a nan gaba kadan, biyo bayan caccakar da ta fuskanta daga kasashen duniya sakamakon dakatar da matan zuwa makarantu da kuma wuraren aiki.

Wasu Mata da ke fafutukar neman 'yancin aiki da karatu a Afghanistan karkashin mulkin Afghanistan.
Wasu Mata da ke fafutukar neman 'yancin aiki da karatu a Afghanistan karkashin mulkin Afghanistan. - AFP
Talla

Kakakin kungiyar ta Taliban Zabihullah Mujahid yayin wani taron manema labarai yau a birnin Kabul ya ce matan za su koma makarantu wani lokaci a nan gaba, ba tare da fayyace takamaiman rana ba.

A cewar kakakin yanzu haka suna tattaunawa kan yadda karatun matan zai ci gaba da wakana da kuma ayyukan da ya kamata su yi a sassan kasar ta Afghanistan bisa matakan kare dokokin addinin Islama.

Sai dai kakakin ya nanata shirin tafiyar da gwamnatin Taliban da Maza zalla ba tare da sanya mata a harkar tafiyar da gwamnati ba, lamarin da ya janyo cecekuce musamman daga manyan kasashen Duniya.

Duk da alkawurran da ta dauka na gudanar da mulki ba tare da take hakkin dan adam ba, akwai fargabar Taliban ta iya komawa turbar yadda ta jagoranci Afghanistan a shekarun 1996 zuwa 2001, lokacin da ta haramtawa mata karatu da aiki, da kuma hana su fita face tare da muharramai, musamman bayan matakan baya-bayan .

Taliban ta bayyana cewa ta na bukatar karin lokaci gabanin kammala tantance yadda za ta tsara karatu da aikin mata da zai yid ai dai da tanadin addinin Islama, inda Mujahid ke cewa zamani ya sauya don haka dole su samar da tsarin da dokokin addini suka amince da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.