Mata za su yi karatun jami'a bisa sharadin rashin cakuda da maza - Taliban
Sabon ministan ilimi mai zurfin gwamnatin Taliban Abdul Baqi Haqqani ya ce za a bai wa matan Afghanistan damar shiga jami'o’i amma bisa sharadin ba za su cakudu da maza ba.
Wallafawa ranar:
Haqqani ya ce tsarin ilimin Afghanistan ya canza sosai tun bayan zangon farko na mulkin kungiyar Taliban, lokacin da aka hana mata zuwa makarantu da jami'o'i.
A farkon wannan wata kungiyar Taliban ta sanar da cewa mata na da damar karatu a jami'a idan suka kiyaye sharadin sanya rigar abaya da nikabi.
Kungiyar Taliban dai tayi ikirarin nisanta kan ta da tsauraran manufofin da ta runguma a zamanin mulkin ta na farko fiye da shekaru 20 da suka gabata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu