Isa ga babban shafi
saudiya - lebanon

Saudiya ta kori jakadan Lebanon tare da kirar nata komawa gida

Kasar Saudiyya ta kira jakadanta dake Lebanon zuwa gida tare da bai wa wakilin Beirut wa’adin sa’o’i 48 ya bar Riyadh, sakamakon abinda ta kira kalaman batanci da wani ministan Lebanon ya yi kan yakin Yemen da take jagoranta.

Yarima mai jiran gadon sarautar Saudiya Mohammed ben Salman yayin wani jawabi a ofishinsa kan taron sauyin yanayi.23/10/21.
Yarima mai jiran gadon sarautar Saudiya Mohammed ben Salman yayin wani jawabi a ofishinsa kan taron sauyin yanayi.23/10/21. via REUTERS - SAUDI ROYAL COURT
Talla

Matakin Saudiya wanda zai kunshi dakatar da shigo da kayayyaki, wani karin koma baya ne ga kasar Lebanon, wacce ke cikin halin matsin tattalin arziki da bankin duniya ya ce mai yiyuwa shine mafi muni a duniya tun tsakiyar karni na 19.

Ma'aikatar harkokin wajen Saudiyya ta ba da umarnin kiran "Jakadanta dake Lebanon zuwa gida tare da  baiwa na Lebanon dake kasar ficewa cikin sa'o'i 48", saboda kalaman da ministan yada labaran Lebanon ya yi a wannan makon.

Sanarwar ta kara da cewa, kasar Saudiya mai arziki ta kuma "yanke shawarar dakatar da duk wasu kayayyakin da kasar Lebanon ta shigo da su daga kasashen waje", saboda " tsaron masarautar da al'ummarta."

Riyadh ta nuna rashin jin dadin tabarbarewar dangantakar da ke tsakaninta da Lebanon inda ta ce za a dauki karin matakai kan birnin Beirut, ba tare da yin karin haske ba.

Martani

Firanmnistan Lebanon Najib Mikati ya mayar da martani cikin gaggawa yana mai cewa ya yi nadamar matakin da Saudiyya ta dauka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.