Isa ga babban shafi
Afghanistan - ta'addanci

Kungiyar IS -K ta dauki alhakin harin da ya kashe masallata 41 a Afghanistan

Kungiyar IS-Khorasan wani reshen kungiyar IS dake Afghanistan ta dauki alhakin harin kunar bakin wake da aka kai a masallacin 'yan Shi'a a birnin Kandahar na Afghanistan wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 41 tare da jikkata wasu da dama.

Cikin Masallacin shi'a da aka kai hari kan masallata a Kandahar  na kasar Afghanistan 15/10/21.
Cikin Masallacin shi'a da aka kai hari kan masallata a Kandahar na kasar Afghanistan 15/10/21. AFP - JAVED TANVEER
Talla

A cikin wata sanarwa da ta fitar kafofinta na Telegram, kungiyar masu da'awar jihadin ta ce wasu 'yan kunar bakin wake biyu ne suka kai hare -hare daban - daban a sassa daban -daban na masallacin yayin da masu ibada ke yin salla a ciki.

Harin ya zo mako guda bayan makamancinsa a arewacin birnin Kunduz wanda shima kungiyar IS ta dauki alhakin kaiwa.

Da farko babban jami’in lafiyar da ke kula asibitin Mirwais ya shaidawa AFP cewa sun samu gawarwakin mutum 33 baya ga wasu 74 da suka samu raunuka a harin.

Akalla motocin agaji 15 suka garzaya yankin da lamarin ya faru don gaggauta ceto rayukan wadanda suka jikkata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.