Isa ga babban shafi
Taliban-Afghanistan

Harin kunar bakin wake ya kashe mutane 41 a Masallacin Kandahar

Taliban ta tabbatar da harin kunar bakin wake yayin sallar juma’a yau a wani masallacin mabiya shi’a da ke birnin Kandahar a Afghanistan wanda ya hallaka mutane 41 tare da jikkata wasu 74.

Harin IS kan masallacin mabiya shi'a.
Harin IS kan masallacin mabiya shi'a. AP - Sidiqullah Khan
Talla

Harin ya zo mako guda bayan makamancinsa a arewacin birnin Kunduz wanda kungiyar IS ta dauki alhakin kaiwa.

Har kawo yanzu dai babu kungiyar da ta sanar da daukar nauyin kaddamar da harin, said ai IS wanda ke matsayin babbar barazana ga Taliban na ci gaba da kaddamar da makamantan hare-haren tun bayan da kungiyar ta kwace iko da Afghanistan a farkon watan Agusta.

Wani jami’in Taliban da ke kula da tsaron yankin, wanda bai bayyana sunansa ba, ya ce bincikensu ya gano cewa, maharin ya tashi bom din da ke jikinsa ne a cikin masallacin lokacin da ake tsaka da sallah.

Da farko babban jami’in lafiyar da ke kula asibitin Mirwais ya shaidawa AFP cewa sun samu gawarwakin mutum 33 baya ga wasu 74 da suka samu raunuka a harin.

Akalla motocin agaji 15 suka garzaya yankin da lamarin ya faru don gaggauta ceto rayukan wadanda suka jikkata.

Majiyoyin Asibitin sun ce mutanen 74 suna karbar kulawar gaggawa don ceto rayukansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.