Isa ga babban shafi
Afghanistan

An kashe mutane 60 a wani hari kan Masallacin Afghanistan

Akalla mutane 60 suka mutu, yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon harin bam da aka kai wani Masallaci da ke birnin Kunduz na kasar Afghanistan.

Masallacin birnin Kunduz da aka kai wa hari a Afghanistan
Masallacin birnin Kunduz da aka kai wa hari a Afghanistan AFP - -
Talla

Wani likita a asibitin birnin ya ce sun karbi 35 daga cikin gawarwakin mutanen da harin ya ritsa da su, tare da wasu karin sama da mutane 60 da suka samu raunuka.

Majiyar Kungiyar Agaji ta MSF ta ce, ita ma ta karbi wasu gawarwaki 15 daga cikin wadanda harin ya ritsa da su.

Wannan shi ne hari mafi muni da aka gani a Afghanistan tun bayan karbe iko da kungiyar Taliban ta yi daga zababbiyar gwamnatin Ashraf Ghani.

Ya zuwa yanzu babu wata kungiyar da ta dauki alhakin kai wannan harin.

Kasar Afghansitan ta kwashe shekaru 20 tana fama da tashe-tashen hankula, sakamakon mamayar da dakarun Amurka da NATO suka yi wa kasar bayan harin ta’addanci 11 ga watan Satumbar shekarar 2001.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.