Kasuwar sabulan da aka samar daga nonon Jaki ta kankama a Jordan
Kasuwar sabulan wanka da aka samar daga nonon Jaki ta kankama a kasar Jordan sakamakon gano amfaninsa da kwararru suka tabbatar.
Wallafawa ranar:
Bayanai sun ce da farko abokai da dangi sun rika yin ba’a gami da dariya ga Iyalan da suka fara sarrafa nonon Jakin a garin Madaba, da ke kimanin kilomita 35 kudu maso yamma da birnin Amman babban birnin Jordan. Sai dai shekara guda bayan haka, kwastomomi sun yiwa kamfanin mai suna 'Atan Donkey Milk Soap' yawa.
Karo na farko kenan dai da aka fara samar da sabulun wanka daga nonon Jaki a Jordan, kodayake tuni nau’in sabulan suka samu karbuwa a wasu kasashen da ke kusa da Bahar Rum.
Kwararru a fagen kwalliya dai sun ce madara ko nonon Jaki na da wadataccen sinadaran da ke taimakawa fata wajen samun kariya daga bushewa, hasken rana, har ma da boye tsufa.
Lita daya na madarar Jaki na samar da sunkin sabulai guda 30.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu