Isa ga babban shafi
Lebanon

Mutane 28 sun mutu sakamakon fashewar tankar mai a Lebanon

Kungiyar bada agajin gaggawa ta kasa da kasa ta Red Cross ta ce, akalla mutane 28 suka mutu yayin da wasu kusan 80 suka jikkata sakamakon fashewar wata tankar mai a yankin Akkar da ke arewacin kasar Lebanon.

Wurin da tankar mai ta fashe cikin dare a yankin Akkar da ke arewacin Lebanon. 15 ga Agusta, 2021.
Wurin da tankar mai ta fashe cikin dare a yankin Akkar da ke arewacin Lebanon. 15 ga Agusta, 2021. AFP - GHASSAN SWEIDAN
Talla

Lamarin ya auku ne a daidai lokacin da al’ummar Lebanon ke fama da matsin tattalin arzikin da ya gurgunta ayyukan asibitocin kasar tare da katsewar wutar lantarki, ba ya ga haddasa matsanancin karancin man fetur a fadin kasar.

Kasar Lebanon
Kasar Lebanon © RFI/Noé Pignède

Kamfanin dillancin labarain kasar at Lebanon ya ce tankar man ta fashe ne bayan kwace ta sojoji suka yi, abinda ya yi sanadin mutuwar mutane 20 da jikkatar wasu 79.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.