Isa ga babban shafi

Miliyoyin mutane a arewacin Amurka sun yi shagulgulan kallon kusufin rana

Miliyoyin mutane ne suka yi dandazo a yankuna da dama na kasashen arewacin Amurka don ganewa idanunsa yadda kusufin rana ya gudana, karon farko cikin shekaru 7 da yankin ke ganin wannan yanayi.

Mutanen yankin na arewacin Amurka sun yi amfani da damar wajen shagulgular murnar ganewa idonsu yanayin.
Mutanen yankin na arewacin Amurka sun yi amfani da damar wajen shagulgular murnar ganewa idonsu yanayin. Getty Images/iStockphoto - Pitris
Talla

Cikin yanayin kada-kade da raye-raye baya ga yin mankas da barasa ne dandazon mutanen da suka kunshi matasa da kananan yara da kuma dattijai ne suka ganewa idonsu yadda kusufin na rana ko kuma dare biyu ya gudana a sassa daban-daban na kasashen Mexico da Amurka da kuma Canada, yanayin da ke zuwarwa yankin karon farko cikin shekaru 7.

Anga dai dandazon jama’ar wuraren shakatawar bakin ruwa na Mexico inda kusufin ranar ya faro zuwa gabar ruwan jihar Ohio na Amurka kana bakin ruwan Niagara da kusufin ya karkare, wanda ya shafe mintuna 3.5 zuwa 4 cikin duhu bakikkirin gabanin washewar gari.

Wasu kananan yara da ke murnar ganin kusufin rana.
Wasu kananan yara da ke murnar ganin kusufin rana. AP - Jake May

Wannan ne karon farko cikin shekaru masu yawa da kasashen ke ganin irin wannan kusufi da ya rufe sararin samaniya baki daya tare da jefa birane a tsananin duhu har na tsawon mintuna, dalilin da ya sanya mutane da dama yin balaguro zuwa sassan da za su fuskanci wannan kusufi tun gabanin zuwansa a jiyan don ganewa idonsu.

A Arkansas anga yadda mutane dubu 30 suka fita kallon kusufin ranar yayinda wasu 400 suka yi amfani da damar wajen daura aure mai cike da tarihi, can a Niagara kuwa da mutane dubu 2 suka fita kallo anga yadda aka daura aure guda 2 da kuma baiko guda.

Yankin na arewacin Amurka ba zai kara ganin kusufi ba sai nan da shekaru 20 masu zuwa.
Yankin na arewacin Amurka ba zai kara ganin kusufi ba sai nan da shekaru 20 masu zuwa. REUTERS - Mario Anzuoni

Mutane sun rika kuwwa cikin murna a lokacin da gari ya kammala dinkewa dif, yayinda aka saki waken R.E.M. na shekarar 1992 mai taken Mutum akan wata.

Niagara kadai ya karbi bakoncin mutane 309 daga Singapore da London wadanda suka yi shiga sanye da wasu kaya masu tambarin rana don bikin kallon kusufin.

Tun bayan shekarar 2017 da yankin na arewacin Amurka ya ga kusufin ranar ba a sake samun yanayin ba sai a yanzu inda kuma hasashen masana ke cewa ba zai sake faruwa ba sai a shekarar 2044.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.