Isa ga babban shafi
amurka

Amurkawa na murnar aukuwar kusufin rana a yau

Miliyoyin al’ummar Amurka na cike da farin ciki, in da suke dakon aukuwar kusufin rana a yau Litinin, wanda manazarta kimiyya suka bayyana a matsayin mafi tsanani da aka gani cikin shekaru 99.

Amurkawa na bukukuwa saboda kusufin rana da za a yi yau a kasar
Amurkawa na bukukuwa saboda kusufin rana da za a yi yau a kasar REUTERS/Beawiharta
Talla

Miliyoyin mnutanen Amurka sun tashi cike da murna saboda kusufin, in da suka yi dandazo a birane da dama, musamman wuraren da duhu zai fi mamayewa a yayin kusufin, wanda aka kira shi da suna “the Great American Eclipse.”

Za a dai fara ganin boyuwar ranar ce a birnin Oregon, in da kuma ake saran yayewarta a South Carolina.

Fiye da mutane dubu 100 ne suka yi dafifi a wani karamin gari da ake kira Madras da ke Oregon, garin da a asali ke da yawan mutane dubu 7, amma ya samu dandazon jama’a yau saboda daga nan ne kusufin zai fara.

Kusufin ya sa Amurkawa shirya bukukuwa da dama a sassan kasar, yayin da cibiyar binciken sararin samaniya ta bayyana cewa, kusufin na wannan karon zai kasance wanda aka fi bai wa muhimmanci a zamanin nan, musamman ma saboda hotunansa da bayanansa da za a dauka.

Tuni aka kirge jami’an tsaro don sauwake wa jama’a cinkoson ababawn hawa kamar yadda jaridar Los Angeles Times ta rawaito.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.