Isa ga babban shafi

An yi kusufin rana a kasashen yankin Amurka

Miliyoyin jama’a ne suka yi dandazo a yankin Arewacin Amurka domin kallon kusufin rana a yau Litinin a daidai lokacin da wata ya rufe daukacin kason rana na tsawon wasu mintina.

People watch the solar eclipse during the Lowell Observatory Solar Eclipse Experience at Madras High School in Madras, Oregon, U.S. August 21, 2017.
An samu duhun kusufin rana a kasashen yankin Amurka REUTERS - Jason Redmond
Talla

Ana hangen kusufin na rana wanda ya faro daga Mexico, ya tsallaka zuwa Amurka, kafin ya ratsa cikin Canada, inda dimbin jama’a masu shawa’ar bai wa idonsu abinci suka taru a wurare daban-daban da suka hada da birnin Fredericksburg da ke tsakiyar Texas, inda ake iya ganin cikakken duhun kusufin.

Kusufin na bana, na daukar tsawon mitina hudu da dakikoki 28, abin da ke nufin cewa, ya fi dadewa fiye da wanda aka gani a shekarar 2017 a sassan Amurka.

Hukumar Binciken Sararin Samaniya ta Amurka NASA ta ce, kusufin rana kan daukar tsawon sakanni 10 zuwa minti 7 ko kuma 12.

Biraren da jama’a ke kallon cikakken duhun kusufin a bana sun hada da  Mazatlan da Mexico da San Antonio da Austin da Dallas da Texas da Indianapolis da Indiana da Cleveland da Ohio da Erie da Pennsylvania.

Sai kuma Niagara Falls da ke  New York da Niagara Falls da ke Ontario da Montreal da kuma Quebec.

Yanzu haka miliyoyin jama’a sun hallara a mashaya da filayen wasanni  da filayen baje-koli da dandali daban-daban domin kallon kusufin ranar a wannan rana ta Litinin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.