Isa ga babban shafi

Wasu barayi sun saci tsabar dala miliyan 30 a Amurka

Duniya – 'Yan Sanda a Los Angeles ta kasar Amurka na can suna gudanar da bincike a kan yadda wasu barayi suka yi sata ta bam mamaki, lokacin da suka kutsa cikin wani ofishin aje kudi inda suka kwashe tsabar dala miliyan 30.

Shugaban Amurka, Joe Biden
Shugaban Amurka, Joe Biden © Mark Schiefelbein / AP
Talla

Baturen ‘Yan Sandan yankin yace an gudanar da satar ce a ranar lahadin da ta gabata, lokacin da ake hutun bikin Easter, wanda aka bayyana shi a matsayin mafi muni a tarihin birnin.

Jaridar Los Ageles Times ta jiyo daga masu gudanar da binciken cewar, barayin sun fasa kan rufin ginin da aka ajiye kudin ne, inda suka kaucewa duk na'urorin dake janyo hankalin jami'an tsaro ko kuma kararrawar tsaro domin satar kudin.

Jaridar tace masu bincike sun bayyana cewar wadanda suka yi satar kwararru ne da suka yi fice wajen sana'ar su, kuma ba'a iya gano satar ba har sai bayan kammala hutun Easter, lokacin da ma'aikata suka bude asusun ajiye kudin dake ofishin.

Wani ma'aikacin kamfanin ya bayyana satar a matsayin ta fitar hankali, ganin yadda wadannan makudan kudade suka bata tashi guda.

Shekaru 2 da suka wuce, wasu barayi sun sace kayan kawar da kudin su ya kai dala miliyan 100 daga cikin motar da aka saka su, lokacin da direbar motar ya tsaya domin hutawa a kan hanyar zuwa bikin baje kolin kayan adon mata a Los Angeles.

A watan Yulin bara, wani barawo ya haka rami ta rufin dakin da ake aje barasa a bakin tekun Venice, inda ya sace giyar da aka yiwa kudi a kan dala dubu 600.

Jaridar Los Angeles Times tace sata mafi girma da aka gani a tarihin birnin, itace na shekarar 1997, lokacin da aka saci dala miliyan 18 da dubu 900 a tashar aje makamai, amma daga bisani an kama barayin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.