Isa ga babban shafi

Macron zai gana da Blinken kan rikicin Ukraine da Rasha da na Isra’ila da Hamas

A yau ne sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken zai gana da shugaban Faransa Emmanuel Macron a birin Paris, game da taimaka wa Ukraine a yakin da take yi da Rasha da kuma rikicin Isra’ila da Hamas a Gaza.

A yau ne sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken zai gana da shugaban Faransa Emmanuel Macron a birin Paris.
A yau ne sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken zai gana da shugaban Faransa Emmanuel Macron a birin Paris. AFP - IAN LANGSDON
Talla

Faransa na daga cikin kasashen da ke samar wa Ukaine makamai, wacce a yanzu ke fuskantar matsalar karancinsu a yayin da take dakile hare-haren Rasha.

Fadar shugaban kasar Faransa ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran kasar na AFP cewa, Blinken zai gana da Macron ne domin tattauna rikice-rikicen da ake samu a wasu kasashe, sannan kuma zai gana da ministan harkokin wajen kasar Stephane Sejourne.

A watan Fabrairun da ya gabata, Faransa ta jagoranci gudanar da wani taron kasa da kasa, a yunkurinta na nema wa Ukraine taimakon kudi da soja, wanda ke cikin batutuwan da shugaba Macron da Blinken za suyi bitarsa.

A ranar asabar da ta gabata, ministan harkokin wajen Faransa Stephane Sejourne, ya ziyarci birnin Cairo na Masar don tattauna batun rikicin yankin Gaza, sannan a jiya litinin ya ziyarci China don bukatarta ta matsawa Rasha lamba kan yakin da take yi a Ukaraine.

Ma'aikatar harkokin wajen Faransa ta ce Sejourne da Blinken za su tattauna batun shirye-shiryen taron kungiyar tsaro ta NATO da za a yi a birnin Washington a watan Yuli mai zuwa, da kuma rikicin da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya da Ukraine da kuma Sudan.

A karshen ganawar tasu, za su jagoranci taron manema labarai na hadin gwiwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.