Isa ga babban shafi

Ƴan sandan Peru sun kai samame gidan shugaban ƙasar saboda agogon ƙatsaita

Hukumomin kasar Peru sun kai samame gidan shugabar kasar Dina Boluarte a wannan Asabar a wani bangare na binciken cin hanci da rashawa da ke da alaka da agogon alatu da bata bayyana cikin kaddarorinta ba.

Shugaban kasar Peru Dina Boluarte yayin halartar tsaron majalisar dinkin duniya.18/09/23
Shugaban kasar Peru Dina Boluarte yayin halartar tsaron majalisar dinkin duniya.18/09/23 AP - Seth Wenig
Talla

Bayanan ‘yan sanda da kamfanin dilancin labaren AFP ya samu gani, ya nuna cewa kimanin jami’ai 40 ne suka kai samamen, domin neman wani agogon kirar Rolex da Boluarte ta yi amfani da shi.

Bata cikin gidan loacin binciken da ‘yan sanda suka ce su na neman kwace agogon ne.

Agogon ƙatsaita

Hukumomi sun kaddamar da bincike kan Boluarte ne tun cikin wannan wata na Maris, bayan da hoton bidiyon wata kafar yada labarai ya nuna ta sanya da wani agogon katsaita kirar Rolex a wajen wani taro.

Samamen na wannan Asabar, wanda aka watsa ta gidan talebijin din kasar Latini, wani aikin hadin gwiwa ne tsakanin 'yan sanda da ofishin mai gabatar da kara.

Hotun bidiyon sun nuna jami'an tsaro kewaye da gidan da ke gundumar Surquillo a Lima babban birnin kasar yayin da aka katse zirga-zirga a hanyar.

Izinin kotun ƙoli

Mai gabatar da kara ne ya bukaci izinin samamen na bazata  da sanyin safiyar Asabar kotun koli ta amince masa.

Hakan ya biyo bayan ne, sakamakon yadda masu gabatar da kara suka ki amincewa da bukatar shugaba Boluarte na karin lokaci don amsa sammacin da aka yi mata na neman ta ba da shaidar yadda ta mallaki agogon hannunta.

Da wannan mataki, Boluarte ta sake tsunduma cikin wani sabon rikicin siyasa tare da kaddamar da bincike a kan ko ta wadata kanta ba bisa ka'ida ba da asusun gwamnati.

Kariya

Ko kuwa kuwa an tuhume ta, ba za ta gurfana gaban kuliya ba har sai bayan wa’adin mulkin ta ya kare a watan Yulin shekara 2026 ko kuma sai an tsige ta, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.

‘Yan jarida da dama ne suka isa gidan shugaban a ranar Asabar amma masu gabatar da kara da jami’an da ke wurin ba su amsa tambayoyi ba.

Ofishin shugaban na Peru kuma bai mayar da martani nan take ba dangane da wannan batu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.